Sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar na kara kudaden makarantun sakandire na gwamnatin tarayya a baya-bayan nan ya janyo cece-kuce da damuwa a tsakanin iyaye da kuma sauran ‘yan Nijeriya a fadin kasar.
Yayin da lamarin ke ci gaba da zama abin jin cikakkun yadda lamarin zai gudana, ga wasu muhimman abubuwa da muka nazarto don samun fahimta game da sabon tsarin biyan kudin makarantun.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ce ta fitar da takardar karin kudin a ranar 25 ga Mayu, 2023. Wannan ya bayyana cewa tsarin ya samo asali ne daga gwamnatin da ta gabata bai mai ci ba.
Bitar karin kudin ta fi shafar sabbin daliban da za su yi rajista a makarantun. A yadda aka saba gani, ana sa ran wadannan daliban za su biya kudade daban-daban, kamar kudin tufafin makaranta.
Takardar ta tabbatar da cewa, har yanzu karatu kyauta ne a makarantun. Karin Kudaden da daliban za su biya ya shafi tsarin tsaftace makarantar da kuma tsare-tsare na bangaren sabbin daliban kwana kadai.
Za a bukaci daliban kwana su biya Naira 30,000 a kowane zangon karatu. An yi wannan tsarin ne don sake inganta ciyarwar daliban. Idan aka yi la’akari da gagarumin tsadar kayan abinci, sannan za a ciyar da daliban abinci sau uku a rana har tsawon kwanaki 80-90 a kowane zango, gwamnati na bayar da tallafin abinci ga daliban kwana marar misaltuwa.
Sabbin daliban kwana za su biya Naira 100,000, yayin da sauran dalibai za su biya N70,000.
Daliban JSS1 da SS1 ne kawai za a bukaci su biya N25,000 na sabbin kayan makaranta, kamar yadda takardar sanarwar ta bayyana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp