Kwanan baya, wata kalma ta shahara sosai a kasar Sin, wato sabon karfin neman bunkasuwa. A watan Satumba na shekarar bara ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wannan kalma, wadda ta janyo hankulan al’umma. A yayin taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS da aka yi kwanan baya, Xi Jinping ya yi cikakken bayani kan wannan kalma.
Ya ce, tushen inganta sabon karfin neman bunkasuwa shi ne yin kirkire-kirkiren muhimman fasahohi ta sabbin hanyoyi da yin amfani da sakamakon da aka samu wajen raya sana’o’i cikin lokaci. Don haka, Xi Jinping ya fidda tsari cewa, ya kamata a gyara da inganta masana’antun gargajiya, da raya sabbin masana’antu da kafa shirin raya masana’antu masu tasowa, da kuma horas da al’umma domin samun masana.
In muka duba tarihi, za a fahimci cewa, tabbas, sabbin sakamakon da aka samu a fannin kimiyya da fasaha, da bunkasuwar tattalin arziki za su taimakawa yunkurin bunkasuwar zaman takewar al’umma da wayewar kan bil Adama. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)