Mujallar “Qiushi” za ta kwallafa wata muhimmiyar kasida ta shugaban kasar Sin Xi Jinping a bugu na 20 da za a fitar gobe Alhamis 16 ga watan nan na Oktoba mai taken “Inganta aiwatar da shawarar ci gaban duniya, da shawarar tsaron duniya, da shawarar wayewar kan duniya da shawarar tsarin shugabancin duniya”.
Kasidar ta jaddada cewa, a halin yanzu, gibin zaman lafiya, da na ci gaba, da gibin tsaro, da gibin gudanarwa na kara karuwa. An gabatar da shawarar kafa kyakkyawar makomar bil’adam ta bai daya, da shawarar ci gaban duniya, da shawarar tsaron duniya, da shawarar wayewar kan duniya da sauransu, domin magance wadannan gibi, da inganta gina duniya mafi kyau, da samar da rayuwa mafi kyau ga al’ummomin duniya. (Amina Xu)