A ‘yan shekarun nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sha jaddada muhimmancin gudanar da wasannin motsa jiki, a lokacin da yara da matasa suke kokarin yin karatu. Ya kuma jaddada cewa, wasannin motsa jiki, muhimmiyar alama ce dake shaida ci gaban zaman rayuwar dan Adam.
A kwanan nan, mukaddashin shugaban hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa ko FISU a takaice, Mista Leonz Eder, ya zanta da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, inda a cewarsa, wani shirin kungiyar da ake kira “Healthy Campus Programme”, wato shirin inganta lafiyar dalibai a makarantu, ya yi daidai da ra’ayin shugaba Xi.
Mista Leonz Eder ya ce, shirin yana shafar daliban jami’o’i, gami da sauran mutanen dake jami’o’in, ciki har da malamai masu koyarwa, da sauran wasu ma’aikata. Kawo yanzu, akwai jami’o’in kasar Sin hudu ko biyar, wadanda suka riga suka shiga cikin shirin, wanda ba wasannin motsa jiki kawai yake mayar da hankali a kai ba, har ma da ba da abinci mai gina jiki da sauransu, shirin da ya yi daidai da ra’ayin shugaba Xi.
Mitsa Leonz Eder, yana da yakinin cewa, wannan shiri zai taimaka ga ci gaban zaman rayuwar al’ummar kasar Sin, da kara kawo musu alfanu. A ganinsa, kasar Sin na da dimbin na’urorin wasannin motsa jiki, da ingantattun shirye-shiryen gudanar da wasannin. Yana kuma fatan kara amincewar al’ummar kasar Sin da wannan shirin na FISU, tare da shiga cikinsa. (Murtala Zhang)