Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin da ya afku a gadar sama ta Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a ranar Juma’a nan da ta gabata.
A cewar hukumar FRSC, hatsarin ya rutsa da wata tirela ce wacce take ɗauke da kayayyaki da fasinjoji.
- Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano
- Gidaje Da Dabbobi Sun Ƙone A Yayin Da Gobara Ta Tashi A Wani Ƙauyen Kano
Binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci wanda aka fi alakƙanta shi da faruwar lamarin. Hatsarin ya rutsa da a ƙalla mutane 71, inda 48 suka samu raunuka, yayin da 23 suka mutu.
Jami’an bayar da agajin gaggawa na FRSC tare da haɗin gwuiwa da rundunar ‘yansandan Nijeriya sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.