Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa, gwamnoni arewa maso gabas sun dukufa wajen ganin sun shawo kan matsalar rashin wutar lantarki da ta ki ci ta ki jinyewa a yankin, a musamman a ‘yan kwanakin nan.
Inuwa ya shaida haka ne ga manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Majalisa Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Wutar Lantarki A Arewa Maso Gabas
- Gwamnan Zamfara Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Daga N7,000 Zuwa N30,000, Za A Fara Biya Daga Yuni
Ya ce, rarraba duk wani abu da ya shafi wutar lantarki ya kasance ne cikin jerin kebabbun hakkoki na gwamnatin tarayya, amma yanzu tun da an samar da sabuwar dokar wutar lantarki, jihohi na iya samarwa da rarrabawa.
Gwamnan ya kara da cewa, “Ko a taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas na karshen nan da muka kammala kwanan nan, mun yanke shawarar cewa kowannenmu ya samar da Megawatts 10 na wutar lantarki daga hasken rana, kuma dukkaninmu muna da damar yin aiki da sabuwar dokar samar da wutar lantarkin, mun san cewa daga yanzu dogaro kan kaifi daya kawai ba zai kai mu ba. Duk abin da muke da shi bai iya fitar da mu daga wannan hali ba”.
Don haka ya tabbatar da cewa yanzu akwai hanya mafi inganci, kuma gwamnonin su na fatan shawo kan matsalar wacce ta dade tana ci wa jama’arsu tuwo a kwarya.
Gwamna Yahaya ya yi wa shugaban Nijeriyan bayanin abubuwan da ke faruwa a Jihar Gombe karkashin jagorancinsa cikin shekaru biyar da suka gabata, da irin tasirin shugabancinsa da kuma kokarin inganta harkokin mulki da ci gaba a matakin jiha.
Gwamnan ya bayyana irin shirye-shirye da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta dauka tun bayan hawansa mulki a 2019.
Ya bayyana irin nasarorin da ya samu a bangarori daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da ababen more rayuwa, da gina al’umma da kuma inganta tattalin arziki.
Ya yi kuma alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru don ganin ta cimma dukkanin shirye-shiryen da ta tsara a cikin sauran shekaru ukun da suka rage mata.