Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaɗu da samun labarin mutuwar mutane 40 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Saminaka, karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.
Hatsarin ya afku ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, 2024 inda wata mota kirar J5 da ke dauke da ‘yan Mauludi ta yi karo da wata motar tirela yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Saminaka domin halartar wani taron Mauludi don nuna farin cikinsu da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
- Remi Tinubu Da Nana Shettima Da Matan Gwamnoni Sun Bai Wa Mutanen Borno Tallafin N500m
- Bukukuwan Mauludi: Wani Mummunan Hatsari Ya Ci Rayukan Mutane 40 A Saminaka
Wasu 48 daga cikin ‘yan maulidin kuma sun samu raunuka a wannan mummunan lamari kuma a halin yanzu suna samun kulawa a asibitoci daban-daban.
Gwamnan ya yi matukar kaduwa da wannan ibtila’in, inda ya ce, “tunaninsa da addu’ar sa na tare da iyalan mamatan da kuma wadanda suka samu raunuka a hatsarin.”
Gwamnan ya umarci kwamishiniyar lafiya ta jihar, da ta tabbatar da cewa, an bai wa wadanda suka jikkata isasshiyar kulawar lafiya.
Gwamnan, ya kara da cewa, gwamnati za ta tallafa wa iyalan mamatan da nufin bayar da taimako don rage musu radadin rashin.