An bayyana gabatar da jam’iyyar African Action Congress (AAC) a Jihar Adamawa domin al’umma ba za su yi nadamar zabenta a 2027 ba.
Sakataren tsare-tsaren jam’iyyar a jihar, Aliyu Umar Doubli, ya bayyana haka ga manema labarai a Yola.
- Ziyarar Shugaba Xi A Serbia Ta Haifar Da Dimbin Nasarori
- Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba – CBN
Ya ce duba da halin matsi da kalubalen da al’ummar Nijeriya ke ciki, jam’iyyar AAC ce za ta fitar da kasar daga halin kunci.
Ya ci gaba da cewa “Al’ummar Nijeriya suna bukatar jam’iyyar mutanen kwarai jam’iyya mai manufofi, manufofin da za su ceto al’ummar wannan kasa daga cikin kunci da kangin talaucin da suke ciki.
“Jam’iyyu da dama suna shirin narkewa su shigo jam’iyyar AAC, kana tsammanin jam’iyyar nan ta fito ne haka kawai? Jam’iyyar AAC ta fito ne don ta ceto ‘yan kasa ta ceto al’umma ta fitar da su daga cikin kangin da aka jefa su.
“An kafa AAC ne domin jama’a, don haka al’umma su zo su hanzarta shigarta, domin jam’iyya ce ta jama’a kuma ana sauraron jama’a ana kuma daukar matakai da ya dace da jama’a don samun sauki da halin kokan da suke yi.
“Wannan sabuwar jam’iyya ce da za ta raba ku da halin kuncin da kuke ciki, ta zo da kyawawan manufofi a kowane fanni, tattalin arziki, kiwon lafiya, Ilimi, harkokin noma da kyautata rayuwar ‘yan kasa” in ji Doubli.
Da yake magana kan batun mafi karancin albashi, Aliyu Umar Doubli, ya ce “Ma’aikaci ya zama abin tausayi, ya zama abin wofantarwa, gwamnati ba ta dauke shi a bakin komai ba, an cire tallafi an kara kudin makaranta, ga tsadar rayuwa, ka fada min mene ne talaka yake mora daga gwamnati?
“Wannan ya sa muke kokarin nuna wa talaka, mu bi duk hanyar da ya kamata domin talaka ya samu sassauci da saukin rayuwa, wannan yanayin ya jefa kasar cikin rashin tabbas, ba a san inda Nijeriya ta dosa ba” in ji Doubli.