Jam’iyyar Labour ta bayyana shawarar hadewar da Atiku Abubakar na PDP ya bijoro da ita a tsakanin manyan jami’iyyun adawa a matsayin shawara mai kyau da ya kamata a yi la’akari da ita.
Sai dai jam’iyyar NNPP ta ce, za ta iya amincewa da shawarar ne kawai idan Atiku zai marawa Rabiu Kwankwaso baya, don kwace mulki daga hannun APC a 2027.
- Gwamnan Jigawa Ya Gabatar Da Kasafin Naira Biliyan N298.14bn Na Shekarar 2024
- Yanzu-yanzu: Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Kano Gobe A Abuja
Mukaddashin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar Labour, Obiora Ifoh, ya ce “Kiran da Atiku ya yi na hadewa a tsakanin manyan jam’iyyun adawa don kawar da jam’iyyar mulkin kama karya abu ne mai kyau da duk ‘yan Nijeriya ya da ce su yi la’akari da shi.
“Kowane dan Nijeriya, yana sha’awar samun ‘yancin dimokuradiyya ta gaskiya. Abin da muke fuskanta yanzu a mulkin APC ya yi nesa da dimokuradiyya. Don haka, idan akwai wata magana da wata jam’iyyar adawa ta kawo don samun ‘yanci, me zai hana a yi la’akari da ita? Duk wani yunkuri ko shawara da za ta sa ‘yan Nijeriya samun ‘yancin Dimokuradiyya, abu ne da muke maraba da shi.”