Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a gaggauta kaddamar da mataki kan yaki da ta’addanci a yankin yammacin Afirka.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wurin taron shugabannin ECOWAS karo na 62 wanda ya gudana a Abuja. Ya kara da cewa akwai bukatar sauya salon yaki da ‘yan ta’adda a yankin yammacin Afirka.
A cewarsa, wannan yunkuri zai karfafa kokarin gwamnatocin yanki wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a yammacin Afirka. Ya yi kira ga sabon tawagar ECOWAS wanda Dakta Omar Alieu Toure yake jagoranta kan gaggauta kammala nazari na sake fasalin kungiyar domin samun inganta yankin yammacin Afirka.
“Dole ne kungiyar ECOWAS ta gudanar da aiki ba dare ba rana wajen ganin an kammala yin nazari kan sauya fasalin ka’idojin shugabanci da na dimokuradiyya a yankin yammacin Afirka, domin karfafa kokarinmu wajen gudanar da shugabanci mai inganci ga kasashenmu.”
Da yake yi wa shugabannin yankin maraba, Buhari ya ce taron wannan shekarar shi ne na 8 da Nijeriya ke shiryawa.
“Dukkan wadannan taruka ciki har da na wannan shekara Nijeriya ce ke shiryawa wanda hakan ke kara karfafa dangantakarmu domin bullo da hanyoyin magance matsalolin kasashenmu da kuma al’ummominmu,” in ji shi.
Shugaban Buhari ya jinjina wa takwaransa na kasar Ghana, Kuffour Addo-Nana wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar bisa shugabancinsa da taya murna ga Shugaban Guinea Bissau, Umaro Embalo kan tabbatar da daukar ragamar shugabancin kungiyar.”
Buhari ya gode wa shugabannin bisa goyon bayansu wajen rawar da suka taka lokacin cutar Korona kan hadin kai yankunan yammacin Afirka.
Tun da farko dai a harabar sabon shalkwatan ECOWAS, Buhari ya nuna godiyarsa ga gwamnatin China bisa tallafin kudade da kayan aiki wajen gina shalkwatan kungiyar.
Gini da aka sanya wa suna idon yammacin Afirka ana tsammanin za a kammala shi ne nan da watanni 26, yana da manyan cibiyoyi guda uku wadanda suka hada da na shalkwatan kungiyar ECOWAS da kotun gungiyar da majalisarta.
A cewar shugaban kasan, “Da ma muna jiran wannan rana tun 10 ga watan Yulin 2019 lokacin da ECOWAS da mutanen China suka rattaba hannu kan kaddamar da kyautar difolomasiyya ga kasashen yammacin Afirka.
A nasa jawabin, Jakadar kasar China a Nijeriya, Cui Jianchun ya ce, “Tallafin gina sabon shalkwantan ECOWAS yana zuwa ne sakamakon kawance da kasar China take da shi da kasashen yammacin Afirka.
“Za mu ci gaba da bunkasa kawance tsakanin China da Afirka, sannan a shirye muke mu bayar da tallafi wajen ci gaban Afirka zuwa mataki na gaba.”