Kwamishinan ma’aikatar sufuri na Jihar Kano, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala ya bayyana cewa aiki tukuru da kyakkyawan niyya na son ci gaban al’ummar Jihar Kano ne ke jagorantar Gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusuf yake ta samun lambobin karramawar daga wurare daban-daban.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida. Ya kuma nuna farin cikinsa bisa karrama na lambar yabo a matsayin gwamna mafi fice a fannin ilimi a Nijeriya, ta hanyar jagoranci da kyakkya-wan shugabanci ta Jaridun LEADERSHIP da Banguard da kuma wasar suka ba ka bai wa Gwamna Abba.
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
- Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
Ya ce wannan karramawar ta cancance shi idan aka yi la’akari da sadaukarwar da yake na jagoranci na-gari da jajircewarsa wajen ci gaban ilimi da sauran fannoni daban-daban a Jihar Kano.
Hon. Ibrahim ya yi nuni da cewa a karkashin jagorancin Gwamna Abba an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkokinsu ba tare da jinkiri ba.
Kwamishinan ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan raya kasa da Gwamna Abba ke yi, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunkasa matasa da bunkasa harkar kasuwanci da sufuri a fadin Jiha Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp