Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), na jihar Kaduna, Kabir Nadabo, ya ce akalla mutane 12 ne suka mutu sannan 28 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Zariya zuwa Kano.
Nadabo ya shaidawa manema labarai ranar Litinin a Kaduna cewa, hatsarin motar ya yi sanadiyar rasa rayuka a kauyen Tashar Yari da karfe 7:36 na safiyar ranar Litinin.
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin ‘Yansanda 3 A Kaduna
- Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutane 5, 10 Sun Jikkata A Hanyar Legas Zuwa Ibadan
“Tirelar mai lamba KTG 454 ZZ tana kan hanyar zuwa Kano lokacin da lamarin ya faru,” in ji Nadabo.
Ya ce abin da ya haddasa hatsarin ya faru ne bisa kuskure da wuce gona da iri, wanda hakan ya zama sanadin asarar rayuka.
Nadabo ya ce, Shugaban Karamar Hukumar Makarfi da Shugaban Tashar Yari sun isa wurin domin duba lamarin.
Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa mutane 40 ne hatsarin ya rutsa da su, inda mutum 28 suka samu raunuka, 12 kuma suka mutu.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin ci gaba da kula da su.
“An sanar da mai motar da ke garin Azare a jihar Bauchi da ya ziyarci ofishin rundunar ‘yan sanda ta Kaduna, yayin da direban tirelar tuni rai ya yi halinsa, shi ma yana cikin wadanda suka rasu,” inji shi.
Nadabo ya yi kira ga masu ababen hawa da su ke bin ka’idojin tuki musamman a kan manyan tituna.