Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya, NCDC ta ce, an samu mutane 5,951 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutane 176 a fadin kananan hukumomi 152 na Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Darakta-Janar na NCDC, Dokta Jide Idris, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja, ya ce bayanan NCDC sun nuna yadda ake ci gaba da samun karuwar masu dauke da cutar a fadin kasar. “Ya zuwa yanzu, wadanda suka fi kamu wa da cutar, su ne ‘yan kasa da shekaru biyar,” in ji shi.
- Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano
- Ɗan Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma Zai Biya Naira Miliyan 10 A Kano
Hasashen ruwan sama a halin yanzu ya nuna cewa, za a iya samun karuwar masu kamuwa da cutar, in ji shi.
Ya bayyana yawan yin bahaya a fili da magudanun ruwa a matsayin abubuwan da ke haifar da barkewar cutar.