Aƙalla mutane 42 da ake kyautata zaton masu Umrah ne sun mutu a wani mummunan hatsari da ya faru da safiyar Litinin, a kan hanyar Makkah zuwa Madina, kusa da Muhras, a Saudi Arabia.
Bas ɗin fasinjojin ta yi karo da wata tankar dizal da ƙarfe 1:30 na dare, lamarin da ya haddasa gobara mai tsanani wacce ta ƙone bas ɗin ƙurmus.
- Saudiyya Ta Ɗauki Nauyin ‘Yan Nijeriya Zuwa Yin Umarah
- Hajjin Bana: Saudiyya Ta Kaddamar Da Kundayen Wayar Da Kai Ga Mahajjata Cikin Harsuna 16 Har Da Hausa
Hukumomi sun tabbatar da cewa mata 11 da yara 10 na iya kasancewa cikin waɗanda suka rasa rayukansu, yayin da mutum ɗaya kawai ake zaton ya tsira, duk da cewa ba a tabbatar da cikakken halin da yake ciki ba.
Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Saudiyya da Red Crescent sun gudanar da aikin ceto a wurin, yayin da aka rufe hanyar na sa’o’i.
Gwamnatin Indiya ta ce ta buɗe layin gaggawa domin taimakon iyalai da tantance gawarwaki, tare da haɗin gwiwar hukumomin Saudiyya.














