An tabbatar da mutuwar mutane bakwai tare da kwantar da wasu 10 a asibiti sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a kauyen Kanye da ke karamar hukumar Kabo a jihar Kano.
Ana zargin cutar ta ɓalle ne sakamakon gurɓataccen ruwa daga wata buɗaɗɗiyar rijiya, wacce ita ce kaɗai al’ummar kauyen ke amfani da ita wajen samun ruwan sha.
- Tallafin Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Buƙaci Gwamnatin Sakkwato Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Biliyan Uku
- Ambaliya: Gwamnatin Yobe Za Ta Tallafa Wa Mutane 25,500 Da Naira Biliyan 1.4
Rijiyar dai ta gurɓace ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya cike wani tafki wanda ya malala zuwa cikin rijiyar.
Nan da nan, mazauna ƙauyen suka fara lura cewa, waɗanda suka yi amfani ruwan sun kamu da rashin lafiya, kuma an sami rahoton mutuwa jim kaɗan bayan haka.
Babban jami’in kula da tsaftar muhalli a yankin, Hafiz Ali Baba ya tabbatar da bullar cutar kuma ya ce hukumomi sun gargadi mazauna yankin da su daina amfani da rijiyar.
Ɓarkewar cutar Amai da Gudawa ta zama kalubalen kiwon lafiya a Kano, musamman jim kadan bayan ambaliyar ruwa.