Akalla mutane 9 ne suka mutu sannan wasu fiye da 800 suka jikkata a yau Laraba sakamakon wata girgizar kasa mai karfin gaske a yankin Taiwan wadda ta lalata gine-gine da dama.
An yi hasashen Girgizar kasar ka iya kaiwa kasar Japan da Philippines kamar yadda tsunami ya yi kafin daga baya a janye batun saboda karfin girgizar.
- An Gano Dajin Da Ya Fi Shekara Miliyan Hudu A Duniya
- Wadanda Suka Jikkata Yayin Girgizar Kasa A Kasar Sin Sun Samu Kulawar Da Ta Dace
Jami’ai sun ce, girgizar kasar ita ce mafi karfi da ta afku a tsibirin cikin shekaru da dama, kuma sun yi gargadin za a kara samun girgizar kasar a kwanaki masu zuwa.
wani masani, mai suna Wu, ya ce, girgizar kasar ita ce mafi karfi tun bayan da aka samu ma’aunin girgizar kasa mai karfin awo 7.6 a watan Satumban shekarar 1999, inda ta kashe mutane kusan 2,400 a wani mummunan bala’i mafi muni a tarihin tsibirin.