Ba a wuce mako guda ba da wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutane 25 a jihar Bauchi, wasu mutane 9 sun sake mutuwa biyar sun jikkata a wasu hadarurruka daban-daban guda biyu a jihar a ranar Laraba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar, Yusuf Abdullahi, ya ce hadarin farko ya faru ne a ranar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023 da misalin karfe 06:25 na safe a kan hanyar Filato zuwa Bauchi.
Ya ce hadarin ya hada da wata mota kirar Toyota Hiace mai lamba KGG 26 LG da kuma Peugeot Boxer (J5) amma ba ta da lamba, dukkansu na kasuwanci ne.
Abdullahi ya kuma bayyana cewa ofishin hukumar FRSC na karamar hukumar Dass ya bayar da rahoton mutuwar mutane hudu, biyar kuma sun jikkata a wani mummunan hadarin mota da ya afku a ranar Laraba.
Hadarin ya rutsa da wata mota kirar Ford Galaxy ce da ake amfani da ita don kasuwanci a karkashin kungiyar NURTW.
Yusuf ya kara da cewa duka wadanda suka jikkata da wadanda suka rigamu gidan gaskiya an kai su babban asibiti da ke Dass.