Tun daga ranar 5 ga wata, aka fara nuna bidiyon dandanon shirin talibijin na murnar bikin bazara na CMG ta kafar CNN, dake Arewacin Amurka, da tashar sadarwar kasa da kasa ta Arewacin Amurka, da tashar sadarwa ta Turai da Gabas ta Tsakiya da Afirka, da kuma tashar sadarwar ta Asiya da tekun Pasifik.
A wannan rana da aka fara watsa bidiyon, sama da mutane miliyan 43 ne suka kalli bidiyon.
Bayanin na nuna cewa, za a ci gaba da nuna wannan bidiyon dandanon shirin talibijin na murnar bikin bazara na CMG har zuwa ranar 18 ga watan nan da muke ciki, lamarin da zai shafi iyalai masu kallon TV kimanin miliyan 400 a kasashen waje. Ban da haka kuma, tun daga 7 ga watan nan da muke ciki, shafin Intanet na CNN da manhajarta, za su kafa dandalin musamman dangane da shirin talibijin na murnar bikin bazara na CMG da kuma al’adun bikin bazarar Sin, domin yada al’adun gargajiyar kasar Sin game da bikin bazara ga jama’ar kasashen waje ta hanyoyi daban daban. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp