Akalla mutane 30 ne da suka tsere daga harin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Birnin Waje da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara suka rasa rayukansu bayan da kwalekwalen da suka hau ya kife a daren Laraba.
Mazauna yankin sun shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, wasu kwale-kwale guda biyu makil da ya dauko mutane wanda yawancinsu mata da kananan yara ne, sun kife a rafin yayin da suke kokarin tsallakawa.
A ‘yan makonnin da suka gabata, al’ummomin karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar sun yi ta samun yawaitar hare-haren da dama. Wasu ‘yan bindiga ne da ake kyautata zaton suna boye a cikin dazuzzukan Gando da Barikin Daji da ke kananan hukumomin Bukkuyum da Gummi ne ke kai harin.
Kwanaki 13 da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun harbe wasu masu ibada 15 bayan wani hari da suka kai a wani masallaci a unguwar Ruwan Jema da ke karamar hukumar Bukkuyum.
A harin na ranar Laraba, mazauna garin sun ce ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai sun mamaye al’ummar Birnin Waje suna harbin mutanen.
Yanayin ya haifar da rudani inda da yawa daga cikin mazauna garin ke ta faman shiga kwale-kwalen domin tsallaka kogin zuwa garin Zauma, wadda ke da nisan kilomita 2 daga yammacin garin Bukkuyum, hedikwatar karamar hukumar Bukkuyum.