Biyo bayan farfasa rumbunan adana abincin gwamnati, wasu matasa biyar sun rasa ransu a jihar Adamawa.
Dama dai jami’an tsaro sunyi amfani da harsasai masu rai, wajan tarwatsa dubban matasan a wuraren da rumbunan abincin su ke.
- Da Dumi-Dumi: Matasa Sun Fasa Rumbun Adana Abinci Na Gwamnati A Adamawa
- Fintiri Ya Sanya Dokar Hana fita Awa 24 A Adamawa
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar matasa akalla 5, da sukayi yunkurin fasa rumbunan abincin dauke da muggan makamai, da suka hada da Adduna, Wukake, Sanduna da Duwatsu.
Yanzu haka dai, hankali ya fara kwantawa, biyo bayan kafa dokar hana fita natsawon awa 24, da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya yi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp