Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Lahadi ya bayyana rasuwar Sheikh Abubakar Giro a matsayin babban rashi ga yankin yammacin Afirka.
Shettima ya bayyana haka ne a garin Argungu na jihar Kebbi, a wata ziyarar ta’aziyya da ya kai a madadin shugaban kasa Bola Tinubu, ga iyalan marigayi Giro wanda ya rasu a ranar 6 ga watan Satumba.
- Gwamna Idris Ya Nada Dan Marigayi Sheikh Giro Mukami A Hukumar Alhazai Ta Kebbi
- Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Babban Malamin Addinin Musulunci Giro Argungu
“Ina nan a madadin shugaban kasa Bola Tinubu, wanda ya kira ni daga Indiya, ya umarce ni da in zo Argungu domin jajantawa iyalan Sheikh da gwamnati da al’ummar Jihar Kebbi da ma Arewa baki daya.
“Wannan babban rashi ne ga jiha, kasa da yammacin Afirka. Marigayi Sheikh Abubakar Giro ya kasance malami mai daraja. Ya yi aiki domin Allah, bai damu da abubuwan duniya ba;l, ya yi rayuwa mai cike da tawali’u.
“Allah Ya gafarta masa kurakuransa, ya ba shi Aljannah.”
A nasa jawabin, Sarkin Argungu, Alhaji Sumaila Mera, ya bayyana cewa masarautar tana alfahari da nasarorin da marigayin ya samu.
Har ila yau, Sheikh Bala Lau, shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah ta kasa, wanda ya karbi bakuncin Shettima a madadin ‘yan uwa tare da sauran jami’an kasa, ya godewa Tinubu da mataimakin shugaban kasa.
Tun da farko da isar mataimakin shugaban kasar ya samu tarba a filin jirgin saman Sir. Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, Gwamna Nasir Idris na jihar ne ya raka shi ta’ziyyar.