Daya daga cikin jaruman fina-finan Hausa da ke haskawa a Masana’antar Kannywood, kuma daya daga cikin masu taka rawa a bidiyon wakokin hausa da ke zagawa a yanzu, ASIYA ALIYU AUTA ta bayyanawa masu karatu babbar nasarar da ta samu game da harkar fim da kuma waka, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arta ta fim da kuma waka. Ga dai tattaunawarta tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Ya sunan jarumar?
Sunana Asiya Aliyu Auta wacce a ka fi sani da Asiya Auta.
Me ya sa a ke yi miki lakabi da Auta?
Sabida ni ce Autar matan gidanmu.
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki.
An haife ni a garin Katsina, ‘Malumfashi Local Gobernment’, na yi karatun firamare a ‘Galadima Primary School’, na yi karatun sakandare a ‘Danrimi Secondary School’, daga nan na tsaya ban ci gaba da karatu ba, amma inada burin ci gaba da karatu, sannan kuma ba ni da aure.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar kannywood?
Gaskiya tun ina karama nake son fim kuma na dauki fim sana’a gaskiyar magana, shi yasa ba na ‘free work’ iya alakata da kai sai ka biya ni zan zo in yi maka aiki.
Wane rawa ki ke takawa a cikin masana’antar kannywood?
Ni jarumar waka ce, sannan kuma jarumar fim na hada duk biyun, kin san an ce gida biyu – maganin gobara.
Tsakanin fim da kuma waka wanne ki ka fara?
Na fara da fim.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Koma miye zai zo maka da sauki idan ka biyo ta inda za ka sami saukin, sabida haka Alhamdu lillah ban sha wata wahala ba.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu kina sha’awar shiga cikin masana’antar, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Dole a kwai kalubale babu wacce za ta ce bata fuskanci wannan kalubalen ba, amma Alhamdu lillah da suka tabbatar da cewa abin da nake so kenan sai suka yi min addu’a da fatan nasara.
Ya farkon farawarki ya kasance?
Gaskiya dai da farko ‘camera’ ta yi min kwarjini dan idan ki ka kula a cikin shirin Rumfar Shehu inda na zo a matsayin kanwar na Braska da kin gani kin san ina tsoron ‘camera’ [Dariya].
Rumfar Shehu shi ne fim dinki na farko kenan?
Eh! Shi ne.
Za ki yi shekara nawa da fara fim?
Zan yi shekara bakwai zuwa takwas 7-8.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Wallahi ko nawa na fada na yi karya ban tuna yawansu ba, ba zan iya cewa ga yawansu ba.
Ko za ki iya fadowa masu karatu kadan daga sunayen finafinan da ki ka fito ciki?
Amaryar Shekara, Dan Talaka, Zabin Raina, Ni da Ke, Ban Gaji Ba, Wata Shari’a, da dai sauransu.
Wane fim ne ya zamo bakandamiyarki a finafinan da ki ka fito ciki?
A’a ni kowane fim ina son shi ba ni da wanda bana so, a ra’ayina na fi son waka fiye da fim.
Ta ya ki ka tsinci kanki a fannin waka?
Waka ita ce abun da ya fi soyuwa a cikin raina, ina son bidiyo na waka sosai, sabida a rana daya za a yi a gama cikin dadin rai babu daukar lokaci.
Ki kan rubuta waka ne ko ki rera ko kuwa iya bidiyon waka kawai ki ke yi?
Bana rera waka bidiyo na waka kawai nake yi.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara bidiyon waka?
Zan yi kamar shekara uku ko hudu 3-4.
Wane bidiyo ne ya fi burgeki ko ya fi baki wuya wajen dauka, cikin wanda ki ka fito ciki?
Bidiyon da ya fi burge ni shi ne; MAGANI, wakar Salim Smart. Bidiyon da ya fi ba ni wahala shi ne; bidiyon wakar ‘DAMA’ ta Sadik Sale, dalilin daya sa ta ba ni wahala shi ne; lokacin da muna yi da an fara aikin sai ruwa ya sauko.
Kin yi bidiyon wakoki sun kai kamar guda nawa?
Za su yi kamar 20 haka, ban da wanda ban tuna ba.
Wakokin da ki ke hawa siya ki ke yi ko kuwa kiranki a ke yi ki zo ki yi a biya ki?
A’a, kira na a ke yi in yi a biya ni.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa