Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewar a yanzu haka har ya fara shirye-shiryen hada kayansa domin komawa garinsa ta asali wato Daura da ke jihar Katsina nan da watanni biyar bayan karewar wa’adin mulkinsa.
Buhari ya shaida hakan ne a ranar Talata a birnin tarayya Abuja sa’ilin da ya amshi bakwancin mambobin Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya), inda ya jinjina wa kungiyar a bisa kokarin da suke yi waje bunkasa hadin kan addinai a fadin kasar nan.
Tawagar kungiyar ‘yan darikar wadanda suka ziyararci shugaba Buhari a karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Khalifa Niass, Khalifan Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya), Buharin ya shaida musu cewa, yana matukar ganin muhimmancin rawar da suke takawa wajen inganta zaman lafiya a kasashen Afrika.
Shugaba Buhari wanda ya gode wa mambobin kungiyar a bisa addu’o’in da suka yi ta yi wa gwamnatinsa da kasa baki daya, kamar yadda hadimin shugaban kansan a bangaren yada labarai Malam Garba Shehu ya nakalto ta cikin wata sanarwar da ya raba wa ‘yan jarida.
Shugaban ya shaida wa bakin nasa cewa yana ta kan kimtsa kayansa da shirin komawa Daura da zarar wa’adinsa ya kare.
A yayin ziyarar, malamin addinin musulunci, Sheikh Tijjani Shehul Hadi Almauritany ya yi wa shugaban kasa da Nijeriya addu’a ta musamman, yayin da kuma Sheikh Abdullahi Lamine ya rero ayoyi daga cikin Alkur’ani Mai girma.
A jawabinsa Khalifan kungiyar, Sheikh Niass, ya yi tilawar tarihin Annabi Muhammad (SAW) da irin darrrusan da ya dace al’ummar musulmai su koya daga rayuwarsa.
Ya nanata muhimmancin tuna ta hakika ga masu aikata laifukan da suka saba wa Ubangiji.
Ya kuma sha alwashin cewa kungiyar za ta cigaba da kokarin hada kan al’umma da bunkasa zaman lafiya kamar yadda addinin musulunci da Annabi Muhammad suka koyar.
Khalifah Niass ya kuma ba da labarin irin kusancin da mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Niass ya yi da Nijeriya da al’ummarta, wanda ya kai shekaru saba’in, inda ya ce iyalin sun kuduri aniyar ci gaba da kulla alaka domin kyautata zamantakewa.