Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa, yafi shugaban kasa Muhammadu Buhari kaunar Nijeriya nesa ba kusa ba.
Gumi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci game da kama Tukur Mamu da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi.
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
- An Kama Mamu Ne Domin Ya Amsa Tambayoyi – DSS
A wa’azin da yake gabatarwa na mako-mako a masallacin Sultan Bello Kaduna, Gumi ya ce, kamata ya yi gwamnati ta nemi afuwa bisa tuhumar Mamu.
Ya ce shi da kansa ya dauki matakin sulhu da ‘yan Bindiga domin a samu zaman lafiya, amma da yawan wasu ba sa son gaskiya.
“A matsayinmu na mutane, bai dace mu nade hannayenmu ba, ba ma yin komai. Na san ayyukan tsaro saboda ni ma daya ne daga cikin ma’aikatan tsaro. Don haka, na san yadda suke aiki kuma na san makircinsu. Ko Sardauna bai kubuta daga makircin su ba, irin su Murtala, Maimalari, da IBB, har da shi kansa Buhari. Dukkansu sun fuskanci makircinsu.
“Kwanan nan, Malam Goni ya fada cikin makircin su; lokacin da wasu matasan sojoji suka hallaka shi. Na yanke shawarar shiga sulhu da ‘yan Bindiga ne don taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.
“Bari in gaya muku, ko shugaban kasa baya kaunar kasar nan kamar yadda nake yi, domin ba ni da wata kasa sama da Nijeriya.” Inji Sheikh Gumi