• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Kamo Hanyar Cika Burina A Harkar Fim -Zainab

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
Fim

A wannan makon mun kawo muku karshen tattaunawar da wakiliyarmu Rabi’a Sidi Bala ta yi da Jaruma Nana Fiddausi Yahaya wadda aka fi sani da Zainab Labarina, ga dai yadda hirar ta kasance.

Ya farkon farawarki ya kasance?

Alhamdulillahi zan ce, saboda lokacin da zan fara an koya min sosai, mutane sun yi na gani har sai da na fahimci abin sosai tukunna aka saka ni.

Ya ki ke ji game da yadda mutane suke ta kace-nace a kanki game da mutuwarki cikin shirin labarina?

Gaskiya abin da zan ce na ji dadi sosai saboda ban san ma haka nake da masoya ba sai da aka kashe ni, na ga maganganun mutane sun yi yawa kan me ya sa aka kashe ni, wannan soyayya ce. Ban ma za ci abin zai kai haka ba, ni kawai dai na san ina son na yi fim, kuma na yi ban za ta daukakar za ta zo da wuri ba, na za ta dai a hankali daukakar za ta zo, to kuma sai ta zo ma a lokaci guda, lokacin ma da baka yi tunani ba. Na hau online na ga mutane suna ta screenshot daga facebook suna ta turo mun, don ni ba na yin facebook. Wani ya ce a nuna ni ko a aljana ce, wani ko a fatalwa ce, wani ko a mafarki ko a tunani, mutane dai na ta magana, to n ji dadi sosai ba kadan ba.

LABARAI MASU NASABA

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

Ko akwai wani kalubale da kika fuskanta tun daga farkon zuwanki masana’antar?

Babu wani kalubale da na taba fuskanta, saboda na shiga masa’antar a mutunce, kuma zan ce na shigo a gata, saboda duk wanda ‘yan uwanka ne suka zo suka yi magana aka saka ka, kuma ka shigo hannu me kyau.

Ya batun nasarori fa?

Alhamdulillahi ana ta samu kuma ana kan samu, yanzu dai aka fara.

Za ki yi kamar wata nawa da fara fim?

Eh! to, farawa har dauka zan wata biyu amma haska shi dukka sati biyu ne da haska shi.Ya ki ka dauki film a wajenki?

Na dauki fim sana’a yadda dan kasuwa zai fita da safe ya je ya yi kasuwancinsa kuma ya dawo da kudi.

Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin hakan wanda ba za ki manta da shi ba tun daga farkon zuwanki Kannywood?

Babban abin da ya faranta min rai shi ne, yadda na samu daukaka da wuri, saboda za ki ga wasu su yi ta wahala su yi ta fim amma daukakar Allah bai kawo ta da wuri ba, amma ni yanayin yadda na zo mutane suka karbe ni kuma aka nuna ana sona sosai to na ji dadin hakan sosai.

Wane ne maigidanki cikin masana’antar Kannywood?

Aminu Saira shi ne maigidana, ni ban da wani maigida da ya wuce shi.

Wace ce babbar kawarki a yanzu cikin masana’antar kannywood?

Gaskiya yanzu a Kannywood ba ni da kawa sai dai kawai wadanda muke mutunci

Idan aka baki zabi cikin ‘yan matan kannywood, wa za ki dauka?

Wadda ta fi burge ni kuma nake so, nake son aikinta, da yanayin rayuwarta, da shigar kayanta, wadda idan ina kallonta a masana’antar ina jin dadi ita ce; Maryam Yahaya, matsayinta na yarinya duk da za ta iya girma ta ko da kadan ne ko shekaru daya ne ko biyu, amma ita ce nake ganin yanzu dai a kannywood yarinya wadda ita ce daidai ni wadda za mu iya hulda ta kawance da ita, ina son ni ma Allah ya sa na zama kamar ita na zama jaruma.

Zabi guda cikin mazan kannywood wanda yake burge ki?

A cikin mazan Kannywood ina son Sadik Sani Sadik ina son shi gaskiya, ina son Ali Nuhu, ina son Adam A. Zango, ina son su da yawa, a matan ma akwai wadanda nake so da yawa.

Ko akwai wanda ya taba cewa yana sonki cikin masana’antar Kannywood?

Gaskiya cikin masana’antar Kannywood babu wanda ya taba cewa yana sona, ban sani ba dai ko a can zuciyarsu ko akwai me sona, kawai dai akwai wanda nake burgewa ni ma suke burge ni na sani. Amma dai wanda zai fito kiri-kiri ya tunkare ni ya ce wance ina sonki da soyayya ko kuma aure a Kannywood dai har yanzu babu.

Kamar yaushe kike sa ran kara yin aure?

Koyaushe ina sa ran yin aure in Allah ya kawo miji nagari wanda nake so yake sona, zan iya yin aure, amma dai kafin nan zan iya cewa ba yanzu ba zuwa gaba, kuma ban ma diba da nisa na ce sai wani lokaci mai tsaho ba, amma a yanzu din gaskiya ba na ji zan iya yin aure.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Nishadi

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales

October 25, 2025
Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
Nishadi

Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 

October 11, 2025
Next Post
AFCON 2023: Abubuwan Da Suka Faru Ga Super Eagles

AFCON 2023: Abubuwan Da Suka Faru Ga Super Eagles

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

November 3, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.