Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, da gangan ya rufe iyakokin kasar nan domin karfafa guiwar ‘yan Nijeriya su iya samar da abincin da za su ci.
Ya ce duk da cewa an soki matakin da farko, amma daga karshe ‘yan Njeriya sun yaba da matakin.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin da yake kaddamar da sabuwar hedikwatar kwastam da aka ce an kashe kusan Naira biliyan 19.6 wajen ginata.
Ginin yana cikin gundumar Maitama da ke babban birnin tarayya (FCT).
Buhari ya ce ya nada Hameed Ali a matsayin kwanturola-janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ne sabida kwazonsa da kwarewarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp