Daya daga cikin fitattun Jaruman, wanda ya shafe shekaru ashirin da biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ALI IBRAHIM wanda aka fi sani da ALI DAWAYYA. Ya bayyana wa masu karatu irin kalubalen da ya fuskanta cikin masana’antar, tare da irin rawar da ya ke takawa a cikin masana’antar ta Kannywood, har ma da wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi sana’arsa ta fim. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ka fara fadawa masu karatu cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.
Sunana Ali Ibrahim wanda aka fi sani da Ali Dawayya.
Me ya sa ake kiranka da Ali Dawayya, shin kana da alaka ko dangantaka da Rukayya Dawayya ne?
Abun da ya sa ake ce mun Ali Dawayya shi ne; Akwai wani fim mai suna ‘Miras A Jo’s’ fim din kamfanin ‘Almah Production’ ni ne ‘light Man’ na fim din, sai janareto din da muke aiki da shi ya lalace na kasa gyarawa, ina ta zurga-zurga duk nayi gumi, sai Ali Nuhu ya ce; “Kanata kaiwa da dawowa ka ki zama, wannan ai kai ne Dawayya, sunan wani fim din Iyan Tama da zai fara”. Shi ne kowa ya fashe da dariya daga nan idan na zo wucewa a lokeshan din sai a yi ta yi mun dan kira ana cewa; “Dawayya”, idan na juyo sai a yi shiru, da’ na fara cewa bana son sunan sai ya zamar mun abun zolaya, amma ba ni da alaka da Rukayya Dawayya sai dai ta sama, da kuma addini daya.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni haifaffen garin Jo’s ne a can aka haife ni, a can nayi karatu daga nan sai ogana dan uwana Ahmad S. Nuhu na zauna a gidan yallabai Ali Nuhu ya taho da ni Kano na fara zama, amma Kano garinmu ne anan aka haifi babana a Dawakin Kudu LGA, cikin Tsakuwa. Bayan na zama dan Kano na fara koyar ‘light’ a wajen Malam Yakubu daga nan na dawo wajan Umar Gotip marigayi, daga nan sai na zama ogan kaina, ina ci gaba da rayuwata. Sai na fara sha’awar Aktin daga nan na zama furodusa na fara fim nawa na kaina mai suna ‘Akhee’, Ajo, Faraga, Sai Na Ga Ali, Kwamachala, Zafin Nema, Kifil Kwallin Mata, Bakauye, akwai uku da na manta.
Idan na fahimce ka kana so ka ce kana da alaka da Ali Nuhu da kuma Ahmad S. Nuhu ta bangaren famili kenan, ko ya batun ya ke?
Eh! ina da shi, Ahmad S. Nuhu unguwar mu daya, kuma akwai auratayya a tsakaninmu da su, shi ne ya kawo ni, Ali Nuhu a gidanshi na zauna har sanda na yi aure kuma Ali Nuhu ya dauke ni kamar shi ya haife ni, ina ci a gidan shi ina sha, sannan kuma ya mun sutura.
Wanne irin rawa ka ke takawa a cikin masana’antar Kannywood, bayan fitowa matsayin jarumi da kuma shirya fim da ka ke yi a yanzu?
Babu irin rawar da bana takawa ni ‘Light Man’ ne kuma Akto.
Za ka yi kamar shekara nawa a cikin masana’antar?
Zan kai kamar shekara 25 tun wajen 1998 na fara.
Ya batun iyaye lokacin da ka fara sanar musu kana sha’awar fara harkar fim, shin ka samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
A’a ban samu matsala ba fatan alkairi suka yi min, amma abokanai na ne kawai idan suka ganni sai ki ji suna mun dan kira wai Akto, haka tun raina yana baci har ya daina.
Bayan fina-finan da ka shirya naka na kanka, ko za ka iya tuna adadin fina-finan da ka fito ciki?
Gaskiya nayi fim zai kai 200.
A wanne fim ka fara fitowa?
Zubaida na kamfanin ‘FKD PRODUCTION’, shi na fara sai kuma wanda suka fito da ni duniya ta sanni.
Wanne rawa ka taka a cikin fim din, kuma ya ka ji a lokacin, musamman yadda ka ke farkon farawa a lokacin?
Sin daya na yi Ahmad S. Nuhu ya zo siyawa Abida Mohammed ‘Prem’ na ‘girft’, gaskiya lokacin da za a sa mun ‘camera’ na ji gabana ya fadi sosai tun da ban saba ba.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta cikin masana’antar?
Gaskiya na samu kam, tun da har gidan yari na je a kan fim dina da na yi furodusin mai suna FARAGA ta dadilin fim din Jarumai 5 ne suka je gidan yari, akwai Mansoor Saddik, Falalu Dorayi, Jibrin S. Fagge, sai ni, sai Tijjani Asase.
Me ya janyo afkuwar hakan?
Na je ‘shooting’ ne wani abokina na ce ya samo min gidan da zan yi aiki, sai ya ce “to”, ashe inda zai samo min ba sa nan sun je kauye, sai ya yi wa abokinshi magana ashe abokin nashi ba shi da inda za a yi aikin sai ya yi wa wani mai gadi magana a kan ya ba mu ‘Guess Hause’ za mu yi aiki, sai mai gidan ya ce an sace masa Pijo da miliyan 10, ya yi mana sharri saboda ya taba neman wata ‘yar fim ta ki yarda da shi shi ne ya huce a kanmu.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa