Aminu Mai Dawayya, ɗaya daga cikin tsoffin mawaƙan da suka daɗe ana damawa da su a masana’antar Kannywood, musamman a shekarun 2010 zuwa 2015, ya bayyana cewa; akwai lokacin da ake gudu idan aka gan shi ya tunkaro wurin da ake ɗaukar fina- finai ko wajen da jaruman masana’antar ke haɗuwa.
A lokutan baya, Mai Dawayya ya tabbatar da yadda duk a cikin mawaƙan da suke faɗin Arewacin Nijeriya, na da da na yanzu; babu wani wanda ya kai shi samun kyautar mota, idan aka cire marigayi Dakta Mamman Shata.
- Samun Kuɗi Ya Fi Samun Ɗaukaka Wahala A Kannywood -Baba Sadiƙ
- Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
A wata hira da ya yi da Radiyon Faransa (Rfi), Mai Dawayya ya bayyana cewa; “Akwai lokacin da idan aka gan ni na tunkaro wajen da jarumai suke zaune, sai a fara guduwa ana cewa, ga ɗan maula nan ya zo”, sannan kuma, abin da mutane da dama ba su sani ba shi ne; babu wani jarumi a Kuduncin wannan ƙasa da Arewacin Nijeriya da ba ɗan maula ba, dukkaninmu da ke ci a wannan masana’anta, babu wanda ba ɗan maula ba.
“Na yi fama da talauci, duk kuwa da irin ɗimbin dukiya da na samu a wannan masana’anta. Don haka, na yi imani da cewa, babu mai yi sai Allah, sannan kuma na yarda da kaƙƙara mai kyau da kuma akasinta”, in ji Mai Dawayya.
A wata hira da Aminu ya yi da Hadiza Gabon a shekarar da ta gabata, Aminu ya ce; “Ba abin mamaki ba ne, idan na ce na samu kyautar mota kimanin guda 75 daga hannun masoyana, kazalika kuma, na sayi kimanin motocin guda 70 da kuɗina, domin kuwa a masana’antar Kannywood, ni ne wanda ya fara hawa motar kansa, haka zalika; ni ne mutum na farko da ya fara zuwa Ƙasar Saudiyya, domin sauke farali”.
Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi.
Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp