Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan wata takaddama da jami’inta da wasu mutane a Unguwan Gangare, Barakallahu a jihar Kaduna.
Lamarin wanda ya faru a ranar 26 ga Fabrairu, 2025, ya yi sanadin mutuwar wani tare da jikkata wasu mutane.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ƙirar Nijeriya Zai Fara Tashi – NASENI
- Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata
A wata sanarwa da kakakin rundunar NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, a halin yanzu wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibitin NAF na 461.
“Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi.
Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp