An kashe mayakan Boko haram da dama a wani harin jiragen yaki tare da lalata maboyarsu a kananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na sojojin saman Nijeriya (NAF), Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar, ta ce, an kai hare-haren ne cikin nasara ta sama a ranar Talata 23 ga Afrilu, 2024.
Gabkwet ya ce, ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kai wa sojojin sashe na 4 na MNJTF hari a garin Lada da ke kan iyaka tsakanin jamhuriyar Nijar da Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp