Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, NAF mai taken ‘Operation Delta Safe’, a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, 2023, ta lalata wasu haramtattun wuraren tace mai a Opu Arugbana da ke karamar hukumar Degema ta jihar Ribas.
Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, haramtattun wuraren, “an gano suna aiki, nan take aka ba da izinin tarwatsa su.”
- An Kashe Mutane 700, An Lalata Kauyuka 50 Cikin Wata 3 A Mazabata — Sanata
- Boss Mustapha Ya Karyata Zargin Satar Dala Miliyan 6.3 Daga CBN
Sanarwar ta ce, duk da lokacin bukukuwan Kirsimeti ne, amma rundunar ta jajirce wajen ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da miyagun ayyuka a yankin Neja Delta da sauran yankuna.
Babban hafsan Hafsoshin sojin sama na kasa, Air Marshal Hassan Abubakar, wanda ya yi bikin Kirisimeti tare da sojoji a yankin arewa maso gabas, kuma a halin yanzu yana jihar Katsina domin gudanar da bikin tare da jami’an Operation Hadarin Daji, ya yabawa kokarin kwamandojin rundunar sojin saman da ke wuraren ayyukansu daban-daban a fadin Nijeriya.
Ya bukaci Hafsoshin da su “ci gaba da kokarinsu da jajircewarsu na fatattakar ‘yan ta’adda da masu tada kayar baya”