Ƙungiyar Hezbollah ta Æ™asar Lebanon, ta naÉ—a Naim Qassem, a matsayin sabon shugaban da zai maye gurbin, daÉ—aÉ—É—en shugabanta Hassan Nasrallah, wanda Isra’ila, ta kashe a wani harin bam a Beirut, a watan Satumba.
Sabon shugaban wanda ya riÆ™e muÆ™amin mataimakin babban sakatarenta, ya kasance É—aya daga cikin jagororinta da suka rage a raye bayan da Isra’ila ta kashe yawancinsu a hare-hare a makonnin nan.
- Boko Haram Ta Hallaka Sojoji 40 A Chadi
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gyara Wutar Lantarkin Arewa Cikin Gaggawa
Sai dai kawo yanzu babu wanda ya san inda yake zaune, duk da cewa ana raÉ—e-raÉ—in cewa yana zaune a Iran, wadda ke taimaka wa Kungiyar.
Cikin sanarwa naÉ—in da Æ™ungiyar ta fitar ta ce ta yi hakan ne bisa dogaro da Allah (SWT), tare da bin tsarin Musulunci, da Æ™a’idar manufofinta, da sharuÉ—an zaÉ“e, ta na mai yi masa fatan jagoranci da alÆ™awarin biyayya ga Allah, da martaba babban jagoranta shahidi Sayyid Hassan Nasrallah da sauran shadidan da ta ce sun rasu.
Ƙungiyar ta Hezbollah, dai ta lashi takobin ci gaba da gwagwarmayarta na yaÆ™ar rashin adalci da zalincin da Isra’ila ke yi har sai ta kai ga nasara.