Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Talata, yayin da yake tsokaci kan tabarbarewar darajar Naira, ya bayyana cewa “mafi mawuyacin halin da aka shiga ya kare” ga matsalar kudin Nijeriya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da gasar zane da kirkire-kirkire ta kasa a Abuja, Shettima, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Stanley Nkwocha ya fitar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, Naira za ta ci gaba da farfadowa a cikin makonni da watanni masu zuwa.
Da yake jawabi a kan matsalolin tattalin arziki, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, “mafi mawuyacin halin da aka shiga ya kare”, inda ya kara da cewa, Naira za ta ci gaba da farfadowa a cikin makonni da watanni masu zuwa, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke magance matsalolin da suka shafi karancin abinci da rashin tsaro.