Mai magana da yawun shugaban tarayyar Najeriya Ajuri Ngelale, ya ce Najeriya na daukar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hulda a fannin raya tattalin arzikin duniya.
Ngelale ya bayyana hakan ne gabanin taron FOCAC dake tafe, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, yana mai cewa, alakar Sin da Najeriya ta ginu ne kan mutunta juna, da zurfafa fahimtar muhimmancin hadin gwiwa na cimma moriya tare.
Jami’in ya ce alakar ‘yan uwantaka ta Sin da Najeriya, da fadadar hadin gwiwar sassan biyu, sun kara fitowa fili karkashin aiwatar da manufofin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, da ma sauran shirye shirye na musayar al’adu tsakanin kasashen biyu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)