Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tattalin Arziki, Tope Fasua, ya bayyana cewa Ƴan Nijeriya za su iya sa ran hauhawar farashi zai sauka zuwa kashi ɗaya cikin ɗari nan ba da jimawa ba, abin da ya yi imani zai sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Fasua ya bayar da wannan tabbaci ne a lokacin da ya bayyana a shirin The Morning Brief na Channels Teleɓision a ranar Talata.
Ya yi bayanin cewa farashin abinci yana fara raguwa yayin da hauhawar farashi ke ƙara saukowa.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
- DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur
Bayanan nasa sun biyo bayan rahoton Hukumar Ƙididdiga (NBS) wanda ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 20.12 a watan Agusta 2025, daga 21.88 a watan Yuli.
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyaki na watan Agusta 2025 ya nuna raguwar kashi 1.76 idan aka kwatanta da watan Yuli.
A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65.
A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka samu a watan Agusta 2024.
Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan, saurin ƙaruwar farashin kayayyaki yana raguwa idan aka kwatanta da watannin da suka gabata.
Dangane da iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Ƴan Nijeriya na “mutuwa da yunwa kullum,” Fasua ya ce:
“Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kawai ya sanya siyasa ce cikin lamarin a ƙoƙarinsa na son ya samu shiga ofishin shugaban ƙasa, ni kuma ba na yin tsokaci a harkokin siyasa.
“Ba lallai bane ya yaba da nasarorin gwamnatin yanzu ba, amma dai ya kyautu mu tsaya kan gaskiya da tabbatattun bayanai.”
Fasua ya amince cewa kashi 20.12 har yanzu babban kaso ne, amma ya jaddada cewa waɗannan lambobin yanzu sun nuna sabuwar ƙididdigar da aka daɗe ana jira.
Ya bayyana cewa: “Hauhawar farashi na kashi 20.12 har yanzu mai girma ne a wasu fannonin tattalin arziki saboda abin da yake nufi shi ne farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa a wasu fannoni, amma ba kamar yadda aka saba ba.
An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su.
“An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai.
Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.”
Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar duniya.