Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sake bayyana a gaban majalisar dattawa tare da magoya bayanta da suka mamaye kofar shiga domin nuna goyon baya a gare ta.
Tun bayan iƙirarin da Natasha ta yi makon a da ya gabata, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakai a majalisar.
- Rayuwata Na Cikin Hatsari, A Dawo Min Da Jami’an Tsarona – NatashaÂ
- PSC Ta Amince Da Ɗaga Darajar Jami’an ‘Yan Sanda 12 Daga Matakin CP Zuwa AIG, Da Sauransu
An yadda a jami’an tsaro ke duba motocin da ke shiga majalisar, sannan ana hana baƙi shiga kai tsaye.
Aƙalla motocin sintiri guda biyar na ’yansanda ne aka girke a bakin kofar majalisar domin tabbatar da tsaro yayin dawowar Sanata Natasha.
Yayin da take magana da ’yan jarida, Natasha ta ce ko da kuwa dakatarwar da aka yi mata ta hana ta shiga da gabatar da ƙadurori, hakan bai hana ta ci gaba da aiki domin ci gaban mazaɓarta ba.
Lauyanta, SAN West Idahosa, ya ce kotu ta tabbatar da cewa Natasha na da damar komawa majalisa ba tare da wata matsala ba.
Amma majalisar dattawa ta dage cewa har yanzu tana nan kan matsayinta na dakatar da Natasha har sai wa’adin dakatarwar ya cika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp