A safiyar yau Lahadi ne na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 ta kasar Sin ta sauka a gefen wata mai nisan gaske, kuma zai tattara samfura a karon farko a tarihin dan Adam daga wannan wuri da ba safai ake gudanar da bincike ba, kamar yadda hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA) ta sanar.
Tare da goyon bayan tauraron dan Adam mai karbar umarni daga kasa, samfurin Queqiao-2, na’urar mai kunshe da bangarorin sauka da tashi ta Chang’e-6 ta yi nasarar sauka a wurin da aka kebe a yankin South Pole-Aitken (SPA).
- Abdul Hamid Dbeibah: Ina Fatan Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Libya Da Sin
- Matar Gwamnan Kebbi Ta Gudanar da Bikin Ranar Tsaftar Jinin Al’ada Ta Duniya A Argungu
Wurin saukar na’urar yana a wani rami na musamman wanda aka sani da Apollo Basin, wanda ke cikin yankin na SPA. Huang Hao, kwararre a harkar sararin samaniya daga kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya ta kasar Sin (CASC), ya ce, an zabi Apollo Basin ne saboda yiwuwar girman darajarsa ga aikin binciken kimiyya, da kuma yanayin wurin da za a sauka, alal misali, yanayin sadarwa da shimfidar wuri da dai sauransu.
Bayan saukarta, na’urar ta Chang’e-6 za ta kammala tattara samfura cikin kwanaki biyu bisa shirin da aka tsara. Za ta yi amfani da hanyoyi guda biyu na tattara samfurin wata, wadanda suka hada da yin amfani da kan mahuji don tattara samfuran da ke karkashin doran wata da kuma daukar samfura a doran wata da hannu na mutum-mutumin inji. (Yahaya)