Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bayyana matukar takaicinsa akan yadda na’urar VAR ta zama marar amfani a Firimiya.
Arteta yayin da ya ke magana bayan kammala wasan da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Newcastle a ranar Asabar, ya bayyana cewar yanzu na’urar VAR ta zama bata lokaci.
Babu wani abu da VAR ke yi a gasar Firimiya domin bai kamata a bayar da cin da Gordon ya yi ba bayan kowa ya gani kwallon ta fita daga cikin fili.
Akwai takaici a ce gasa kamar Firimiya da babu kamarta a Duniya, a ce ana tafka irin wannan babban kuskure. inji Mikel Arteta.