Masana kimiyya na kasar Sin sun gano cewa, falalen dutsen cikin duniyar wata da ke yanki mai nisa ya fi tsananin sanyi fiye da na yanki na kusa. Sun bayyana hakan ne bayan yin nazari kan samfurin kasa na yankin mai nisa da na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 ta kasar Sin ta dauko daga can.
Wannan binciken ya bayar da shaida game da yanayin samuwar duwatsu da sinadaran da suka hadu suka zama kasa da albarkatunta domin gano bambancin yanayin zafi a tsakanin yankin wata na kusa da kuma na nesa, inda hakan ya bayar da muhimman bayanan da ake bukata don fayyace samuwar halittar wata.
Cibiyar binciken sinadaran Uranium na karkashin kasa ta Beijing, da Jami’ar Peking da Jami’ar Shandong ne suka gudanar da binciken, kuma aka wallafa a cikin mujallar nazarin kimiyyar dabi’ar halitta ta “Nature Geoscience”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)