Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon nazari da aka yi kan mutane 2,500 a fadin kasashe 10 na Latin Amurka. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, masu bayar da amsa sun amince da manufa da nasarorin da aka cimma na zamanantar da kasar Sin, tare da gamsuwa da dangantakar Sin da kasashen Latin Amurka. Al’ummar Sin da Latin Amurka mai makoma ta bai daya na kara samun goyon baya daga mutanen yankin Latin Amurka.
Kasashen Sin da na Latin Amurka dukkansu masu tasowa ne kuma muhimman abokan hulda dake hadin gwiwa bisa daidaito da moriyar juna da neman ci gaba na bai daya. Manufar zamanantar da kasar Sin ta ba kasashe a Latin Amurka wani misali mai daraja yayin da suke kokarin neman ci gaba. Nazarin ya nuna cewa, galibin wadanda suka bayar da amsa na da kyakkyawan ra’ayi game da kasar Sin, inda kaso 94.8 ke ganinta a matsayin wadda ta samu nasara. Kaso 85.9 kuma suna sha’awarta, sannan kaso 94.8 na kallonta a matsayin wadda ke da karfin tattalin arziki, sai kaso 91 da suka yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka cikin lokaci mai tsawo.
A matsayinta na mai ingiza hadin gwiwar Sin da Latin Amurka, tasirin shawarar Ziri Daya da Hanya daya a kasashen Latin Amurka yana karuwa, kuma yadda masu bayar da amsa suke fahimtar shawarar, shi ma yana karuwa. A bayanin shawarar, masu bayar da amsa sun bayyana ra’ayinsu game da muhimman batutuwa 3 dake cikin yarjejeniyar shawarar, inda matsayin shawarar na samar da wani tsari da kasashe za su runguma domin inganta tattalin arziki ya samu goyon baya da kaso 55. Matsayinta na wani muhimmin abu da Sin ta gabatar domin kyautata tsarin jagorantar harkokin duniya ya samu kaso 54, yayin da burin Sin na hada gwiwa da sauran kasashe ya samu kaso 52.6. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp