A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a. Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin.
A shekarar 2024, mizanin aikin yi da na farashin kayayyaki sun kasance kan wani mataki mai daidaito, inda aka samar da guraben ayyukan yi miliyan 12.56 a birane, kana kudin shigar kowanne dan kasa ya karu da kaso 5.1. Baya ga haka, an karfafa tsare-tsaren bayar da ilimin tilas da kula da tsoffi da kiwon lafiya da sauran harkokin al’umma.
Cikin nazarin da CGTN ta gudanar, masu bayar da amsa sun yaba matuka da ingancin shugabancin gwamnatin kasar Sin, inda kaso 78.8 suka ce an cimma gagarumar nasara a harkar bayar da ilimi, kaso 70.1 sun yaba da yadda aka samu karuwar kudin shigar jama’a, kaso 63.4 kuma, sun yaba ne da ingantuwar muhallin rayuwa. Haka kuma, kaso 61 sun yaba da ingantuwar tsarin kiwon lafiya yayin da kaso 58.1 suka yaba da ingantuwar yanayin muhallin halittu. Wasu kaso 62.7 kuma sun ce fa’idojin da manufofin Sin ke da su na da muhimmanci wajen bayar da tabbaci ga ingantaccen tsarin shugabanci a kasar.
An samu wadannan alkaluma ne daga nazarce-nazarce biyu da kafar CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun cibiyar bincike kan harkokin kasa da kasa a sabon zamani, inda suka mayar da hankali kan “Yanayin Zama a Kasar Sin” da “Zamanatar da Kasar Sin”. Masu bayar da amsar sun hada da mutanen yankin arewacin Amurka da nahiyar Turai da Afrika da Oceania da kudu maso gabashin Asiya da gabashi da kudu da tsakiyar Asiya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp