Mataki na farko da ake dauka idan za ayi maganin matsala shine a amince da cewar akwai matsalar, da kuma yarda da irin halin da za a shiga wajen nemo amsar da ta dace da matasalar.
Bugu da kari sai mutum ya samu bayanai ta hanyar tambayoyi da bincike, domin samun matsaya daganan sai a samu mafita ko maganin matsalolin.
- Xi Zai Halarci Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
Mataki na kashe shine mutum ya samu matsayar da take bata karshe ba wanda za’a iya gwada shi ta fannoni daban- daban, a duk tsawon lokacin da ake aiwatar da shi tsarin, wanda hakan ne zai sa a wata matsayar da za’a dogara da ita da za ta taimaka matuka gaya (Ahmed, 2005).
Wannan dabarar ta danganta ne da yadda shi Malamin zai gabatar da misalan zuwa ga daliban, yi masu bayanai da tattaunawa tare da su, zuwa har a kawo lokacin da su daliban za su rika bada tasu gudunmawa.An san wannan dabarar koyarwar a matsayin daya daga cikin yadda ake shiga cikin lamarin ta hanyar sa kai ta hanyar lura da yadda lamarin yake.Abin ya shafi farawa da wani abu daga ciki har ya zuwa ga abin gaba daya, daga misalan har ya zuwa ga tambayoyin,ko kuma daga wani abu daga ciki zuwa gaba daya,domin samun cimma matsaya da zata taimaka,ta hanyar yin nazari abubuwan da suke isassun abubuwan da za su amfanar, da kuma samun damar gamsassun bayanan da za su taimakawa wajen yin doka, yadda za ayi doka, ko kuma wata matsaya mai amfani. Koyo ta hanyar gabatar da mutum shine hanyar mafi dacewa, saboda tana taimakon mai koyo ya kasance ya yi abubuwa nau’oi daban- daban na ilimi. (Aziz and Khaled, 2012.).
Dabarar koyo ta hanyar bincike na da hanyoyi daban daban wadanda aka fi sani da amfaninsu sun hada da (Ahmed, 2005):
1)Malami yana zabar da za’a gane abinda da aka koyo sosai da sosai.
2)Malamin yana yin bayani na hanyar da aka bi ga sun daliban da suke cikin aji, da irin cigaban da aka samu na gane matsalar.
3)Dalibai suna yin tambayoyi domin su samu mafita . 4. Daibai suna zabar hanyoyi daban- daban daga nan kuma su gano yadda al’amarimn yake.
4)Daibai suna tattauna dokokin ko gano abubuwan da suke da nasaba da shi lamarin da tunanin yadda za su gano abin.
5)Dabararr yin bincike wata hanya ce da ake sake duba yadda take,daiban suna tattaunawa akan matakan saboda su gano yadda za suyi maganin matsalar.
Dabarar koyo ta gane yadda abin
Na daya daga cikin dabaru na zamani wadanda suka yi bayan ikan da akwai bukata a taimakawa wajen abin ya zama mai amfani ga wanda yake koyo, ta hanyar koyarwa da koyo, ya kasance shi ke neman ilimi ya kuma gano shi da kan shi.Amfanin Malami shine ya bada kwarin gwiwa, sawa a hanya, da samar da hanyoyin da suka dace.Ta dabarar shi dalibai suna kara samun kwarin gwiwa su amince da kansu wajen gano dabaru da kuma yadda za ayi maganin matsaloli.Irin hakan yana nuna akwai gamsuwa da kausashi na son cigaba da koyo, koyo da kuma gano sabbin dabaru su d kansu ba tare da taimakon wani ba. Ana kiran irin hakan sunaye daba daban, da suka hada da dabara ta abinda mutum yake yi idan yana son ya koya,ganowa, koyo da cimma buri,a samu wani bayani na abinda ake bukata. (Aziz and Khaled, 2012).