Na karshe kan wannan maudu’in
7.Dabarar tattaunawa ta magana a bangaren karatun digiri na biyu hakan na taimakawa yadda daliban da ake koyamawa za su iya nazari,da gane yadda za su ji matsalolin ta hanyar amfani da binciken kimiyya.
Daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci wadanda suka kamata a kula da su lokacin da za’ayi amfani da dabarun koyarwa ta bayani sun hada da wadannan abubuwan.
- Bankin Duniya Da IMF Na Kassara Tsarin Ilimin Jami’o’i A Nijeriya – ASUU
- Sin Da Brazil Da Afrika Ta Kudu Da AU Sun Kaddamar Da Shawarar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Don Baiwa Kowa Damar Cin Gajiyar Ilimin Kimiyya
1.Bukatar shiryawa da zama dole dangane da darasin ta wannan hanyar, saboda maganar gaskiya abin miuhimmancin da ya shaf ilimi da abinda darasin ko maudu’in ya kunsa, hanyoyin da za’ayi da suka hada da yadda shi Malamin da daliban za su tafiyar da lamari wato yadda zai koya masu da kuma yadda yake bukatar abinda suka koya ya amfane su.
2.Bayyana abubuwan da su daliban za su yi:,hakanan ma abubuwan da shi Malamin za iyi, kai har ma da yadda za’a tafiyar da shi lamarin da zai bada dama ta tattaunawar.
3.Sa ido ko lura lokacin da ake yin tattaunawar, domin ta hakan ne su daliban za su kara maida hankali kan abubuwan da ake koya masu, suna kuma iya yin tambayoyi da kuma sa ido da lura, ba tare da sai sun tashi daga inda suke zaune ba, saboda kada su samar da wata matsala.
Kammalawa
Wannan karatun ko darasin da aka koyar akwai abubuwan da aka karu dasu wadanda suka fi muhimmanci sune:
1.Hanyar koyarwa wata kimiyya ce da take da hanyoyinta da kuma dokoki, wadanda ana iya lura da su, ayi Nazari, magana kan yadda suke ,daga nan kuma sai a koyi darussan.Magana kan dacewar Malami wajen amfani da dabarun koyarwa, abin na iya sanadiyar bunkasa ilimi gaba daya abinda ya hada da bincike- binciken da ake yi domin cimma burin.
2.Koyarwa na da hanyoyin da ake yenta wadanda suka fi muhimmanci sune lacca,tattaunawa, zama kan kujerar zama ta jagoranci kan abinda za’ ayi, musayar ra’ayi, da dai sauransu.
3.Dabarar koyarwa ta lacca irin wadda ake yiwa dalibai tana da matukara amfani, wadda ta fi mafani ita ce tana bukatar Malami ace ya san lamarin lokacin da yake shirya darasin da kuma gabatar da shi, wajen yin amfani da abubuwan da suka hada da wasu abubuwan da za’a iya gani a fuska,yadda idanu suke kasancewa,yadda murya take kasancewa da darasin da ake yin magana akan darussan da ake ayi wadanda basu da muhimmanci shi ne yadda shi Malamin yake iya kokarinsa wajen ayyana abubuwan da ake cimmawa, da kuma aikin sa yayi bayani da daidaita duk wani abinda ya shigewa masu koyo duhu.
4.Dabarar koyarwa ta musayar ra’ayi tana daya daga cikin dabarun koyarwa masu kyau saboda yadda take da amfani a cikin aji,saboda yawan tambayoyi da Malami yake yi lokacin yin mu’amalar shi da dalibai,domin shine yake bada amsoshi ta mafani da ma’anoni daban- daban.
5.Babbar kujerar da ake da ita ma wata dabara ce ta koyarwa, inda ake koyo ta hanyar bincike, ganowa, tattaunawa,da kuma sauran dabaru ana amincewa da su, saboda suna bukatar hadin gwiwa ne tsakanin Malami da daliban shi, inda shi ma zai karfafa masu niyyarsu su yi bincike, tunani, da kuma gano yadda lamarin yake.
Wannan shine na karshe cikin ikon Allah kuma mako mai zuwa za mu fara kan maudu’in daya shafi ‘amfanin tsarin yadda Malami zai koyar.’