Dokar ba da izinin tsaron kasa wato NDAA ta shekarar kasafin kudi ta 2025 ta kasar Amurka na ci gaba da bibiyar matsayar adawa da kasar Sin, wanda ke nuna wani kuduri mai cike da husuma maimakon hadin gwiwa. Dokar wacce aka tsara a matsayin wata kariya ga tsaron Amurka, tana cike da tanade-tanade da nufin bata diyaucin kasar Sin da murkushe bunkasar tattalin arziki da fasaha. Babu inda wadannan tsangwama suka fito fili, ko kuma suka fi hatsari, kamar yadda Washington ke katsalandan a harkokin da suka shafi yankin Taiwan na kasar Sin.
Yankin Taiwan ya zama abin rikewa a dabarun Amurka wajen tinkarar kasar Sin, duk da cewa a bainar jama’a ta tabbatar da kudurinta na mutunta ka’idar Sin daya tak a duniya. Sanya sayar da makamai ga Taiwan da hadin gwiwar tsaro a cikin NDAA yana wakiltar kalubale kai tsaye ga ’yancin kasar Sin, da kuma dagula wani muhimmin batu da kasar Sin ta dade tana bayyana a matsayin jan layi. Amurka ta lullube aika-aikarta da ikirarin kare dimokuradiyya, amma a zahiri manufarta ta tayar da zaune tsaye ta hanyar mayar da Taiwan wani sansanin makamai masu tarin yawa ta fito fili karara. Kasar Sin tana tsayin daka kan martanin da take mayarwa game da wadannan tsokana, kuma ta ci gaba da yin kira da a mutunta juna da zaman tare cikin lumana tare da nuna aniyar yin aiki tare yadda ya kamata, duk da cewa Amurka na ci gaba da nuna kiyayya da gaba ga Sin.
Hakazalika, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta yi watsi da ra’ayoyinta na nuna kiyayya da kuma mutunta jajayen layukan kasar Sin, ta kuma ba da shawarar samar da tsari na bai daya dake ba da fifiko kan warware sabani ta hanyar tattaunawa. Batun Taiwan na iya zama abin koyi wajen sassanta sabani ta hanyar fahimtar juna. Amma duk da haka Amurka ta bayyana niyyar yin amfani da batun a matsayin madogara na ci gaba da neman tsokana.