Jami’an hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi reshen jihar Legas sun bankado hodar Ibilis da kudinta ya kai naira biliyan 4.5 a cikin kayan abincin yara na kamfanin Nestle Cerelac a filin ta shi da saukar jiragen sama na Kasa da Kasa na Murtala Muhammed da ke jihar Legas.Â
A cikin sanarwar da kakakin yada labarai na hedikwatar hukumar, Femi Babafemi ya fitar ya ce nauyin Hodar ya kai kilo 23.55.
Sanarwar ta kara da cewa, Jami’an hukumar sun kuma kama wani tsohon Direban kamfanin Bas na BRT, Muyiwa Babalola Bolujoko a filin jirgin ya hadiye ledar hudar Ibilis 90 inda jami’an suka tilasata masa yin kashin su.
A cewar sanarwar an kama shi ne a wajen tantance kaya a filin jirgin a yayin da yake shirin hawa jirgin Qatar Airways don balagoro zuwa Doha da Sharjah inda zai tsaya a Dubai.
Sanarwar ta kara da cewa sun kuma kwace wasu kayan maye da nauyinsu ya kai kilo 2,453.65 da aka shigo da su daga gabas ta tsakiya da kuma kasar Amurka.
A cikin sanarwar kayan wadanda aka biyo da su ta kasar Afika ta Kudu an shigo da su ne a ranar 29 ga watan Yunin 2022.
Sanarwar ta ce an kuma kama wata mata ‘yar shekara 68 a jihar Ribs bisa safafar tabar Wiwi da nauyinta ya kai kilo 231.2.