Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ta Ƙasa ta kama wasu masu baburan kai saƙo uku a Abuja bisa zarginsu da rarraba haramtattun kayayyaki a faɗin birnin.
Waɗanda ake zargin: Sabo Sule, mai shekaru 24; Samuel Nnamdi, mai shekaru 28; da Idris Jibrin mai shekaru 28, an kama su ne a lokacin da jami’an tsaro suka gudanar da bincike a yankunan Gwarimpa, Jahi, da Galadimawa a Babban Birnin Tarayya.
- Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji
- Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar, ta ce an ƙwato jimillar giram 149.8 na Canadian Loud, wani nau’in tabar wiwi, daga hannun waɗanda ake zargi da amfani da babura da aka saba yin aikin kasuwanci.
“Jami’an Babban Birnin Tarayya Abuja suka gudanar da bincike a yankunan Gwarimpa, Jahi da Galadimawa, sun kama wasu matuƙa babaran kai sƙo guda uku: Sabo Sule mai shekaru 24 da Samuel Nnamdi mai shekaru 28 da Idris Jibrin mai shekaru 28 da laifin rarraba haramtattun kayayyaki a cikin birnin. Jimillar tabar wiwi 8, Loud guda 149 daga Ƙasar Canada. su,” in ji shi.
Babafemi ya kuma ce jami’an ‘yansanda sun kama wasu kayayyaki na hodar iblis da kuma tramadol 225mg da aka boye a cikin madubin mota 71 da aka tura zuwa Birnin Libreɓille na Ƙasar Gabon ta hanyar da ake fita a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas.
Ya ƙara da cewa an kama aƙalla mutane uku da ake zargin suna da alaƙa da kayan a wani samame da aka kai musu.
Babafemi ya ce, “Kashi na farko na kayan, wanda ya kunshi kwayoyin Tramadol 57,420 na tramadol 225mg da 57 na hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.60, an kama su ne a cikin wani kaya da zai je kasar Gabon a Air Cote d’Iɓoire a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli, 2025. Wani shahararren dan kasuwan nan mai suna Benkwee Ihesi Osina, shi ne wakilin cargo, wanda aka kama. Shipment, an kama shi nan take, wani bincike ya kai ga kama wani wanda ake zargi, Uzochukwu Godspower Chukwurah, a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli.
“An gano fakiti 11 na hodar iblis da nauyinsu ya kai kilogiram 1 daga baya daga wasu madubi guda hudu da ake shiryawa don fitar da su zuwa kasashen waje, wadanda aka gano a gidan Uzochukwu a ranar Litinin, 21 ga watan Yuli, wanda ya kawo adadin hodar iblis zuwa 68 mai nauyin kilogiram 2.60.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp