Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama akalla mutane 192 da take zargi da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Satumba a Ebonyi.
Kwamandan hukumar, Mista Iyke Uche na jihar, a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abakaliki ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma kama kimanin kilogiram 113.414 na tabar wiwi.
Ya kara da cewa, an kuma kama 0.0621kgs na methamphetamine, wanda aka fi sani da Mkpurummiri, a yayin da jami’an hukumar su ka kai wani samame.
Dangane da batun fataucin miyagun kwayoyi a jihar, kwamandan ya ce Ebonyi tana da karancin wuraren sana’ar ta’ammali da miyagun kwayoyi amma tana da yawan masu amfani da kwayoyin.