Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ta samu nasarar cafke wani tsohon Soja mai shekara 90 a duniya, Usman Adamu bisa zargin safarar miyagun kwayoyi wa ‘yan bindiga a Sokoto.
A wata sanarwar dauke da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na NDLEA, Mista Femi Babafemi ya ce, an kama tsohon sojan ne a ranar Laraba a garin Mailalle da kw karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Ya ce sun kama Usman ne da tabar wiwi mai nauyin 5.1kg.
Baya ga wannan, a ranar Alhamis, hukumar ta kama wata mota a JIhar Zamfara makare da kwayar Diazepam 50,000 a kan hanyarta ta zuwa Sokoto daga birnin Benin na Jihar Edo, wanda ta ce mallakar wani ne mai suna Umaru Attahiru.
Wakilinmu ya nakalto cewa NDLEA ta kuma damke wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong da duro uku na kwayar crystal methampetamine – wadda ake kira Mkpuru Mmiri a Nijeriya.
Kayan da NDLEA ke zargin an shiga da su ne daga Indiya, an kama su yayin da ake shirin kai su wani wuri a birnin Legas lokacin da aka tare motar da ke É—auke da su.