Hukumar da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta gurfanar da wasu ‘yan kasar Philippine 11 a gaban Babbar Kotun da ke a jihar Legas bisa zargin su da shigo da Hodar Ibilis cikin Nijeriya da nauyinta ya kai kilogiram 13.65.
Jami’an hukumar sun kuma cafke Jirgin ruwan su mai lamba MV Karteria inda aka gurfanar da su a gaban kotun kan tuhuma hudu ta hada baki da shigo da kayan ta haramtacciyar hanya da kuma safarar miyagun kwayoyin da aka hana shigowa da su cikin kasar nan.
Wadanda ake zargin an cafke su ne a ranar 7 ga watan Nuwambar 2021 a tashar Jiragen Ruwa ta GDNL da ke a jihar Legas inda aka bayar da umarnin a aji ye su a gidan gyara hali har zuwa lokacin da mai Shari’ar Alkali Nicholas Oweibo zai yi masu shari’a.
Wadanda ake zargin su ne, Gerapusco Fidel; Antolin Reynante; Bechayoa Edgar; Voltaire Tejero, Kent Ryan; Bryan Kamos; Ralph Christopher; Maningo Dennis; Romnick Albarracin; Ervin Pabuaya da kuma Quetua Judezar Sevilla.
Alkalin kotun mai shari’a Oweibo ya dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Yunin 2022.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp