Hukumar da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kaduna ta sanar da cewa, ta rushe mashaya 14 da ake sayar da kayan Maye tare da cafke ‘yan Maye 100 a cikin mako hudu da suka gabata a jihar.
Kwamdan hukumar na Kaduna Umar Ardo ne ya bayyana hakan a hirarsa da Kamfanin dillancin labarai a Kaduna inda ya ce, Jami’an hukumar ne suka rushe mashayar a jihar Kaduna da kuma garin Zaria a watan Mayun 2022.
Mashayar da aka rushe akwai ta Abakwa, Malali, Tirkaniya, Rigasa, Romi, Filin Minista, Chikaji, Sabon Gari da sauransu, inda ya kara da cewa, mashayan da aka cafke, sun hada da maza 93 sai kuma mata 7.
Umar ya Kara da cewa, Jami’an sun kwace kayan maye kamar su, Tabar Wiwi mai nauyin kilogiram 192.54 da hudar Ibilis da sauran kayan Maye.